Saturday, 23 September 2017

Hadiza Gabon Ta CaccaKama Wani Masoyinta Magana A Shafinta Na Twitter



Hadiza Gabon Ta Tayi aman Wuta Ga Masu Kiran Ta Da Ta Yi Aure.

“Toh ko zaka baiwa tsoho shawaran yayi ma tsohuwa ritaya ya kawo ni ne? ”Amsar da jaruma Hadiza Gabon ta baiwa wani mai kiranta da tayi aure, a shafinta na Twitter kenan.

Jarumar ta bayyana cewa ta gaji da yawon damunta da akeyi da tayi aure tayi aure, wannan kuma shi yasa ta gagara rike fushinta a yayin da taga wannan kiran.

ArewaBlog.Com



Monday, 4 September 2017

Video] Kalli Yadda Wata Mata Ta Cinye Naman Sallar Ta Gaba Daya

Me yayi zafi haka, wata Mata Ta Saka naman rago guda ta cinyeshi a lokaci daya...Ku Danna download video Dake Kasa Domin Sauke Videon


Download now 

https://www.youtu.be/-09dZQhEotU


Source arewarmu


Sunday, 3 September 2017

Karanta ka karu: Ko kun san Jihar da ta fi yawan ma'aikatan gwamnatin tarayya a Najeriya?

Gwamnatin tarayya ce gaba a bangaren samar da ayyuka a kasa. Duk lokacin da gwamnatin tarayya za ta dauki aiki ta kan yi raba dai-dai ne tsakanin jihoshin Najeriya. A wata kididdiga da tsohon shugaban sashen kula da bunkasa ayyukan gwamnatin tarayya, Dakta Joe Abah, ya fitar ta nuna adadin jimillar ma'aikatan gwamnatin tarayya da ke karkashin ma'aikatun tarayya da kuma kason da kowacce ke da shi.

Ga adadin ma'aikatan da kowace jiha ke da su da kuma jimillar ma'aikatan kamar yadda Joe Abah ya wallafa;

Jihar Imo 5825, Jihar Kogi 5186, Jihar Ogun 4669, Jihar Delta 4419, Jihar Akwa Ibom 4416, Jihar Benue 3951, Jihar Edo 3890, Jihar Abia 3579, Jihar Anambra 3576, Jihar Kaduna 3199, Jihar Ondo 3393, Jihar Oyo 3244, Jihar Osun 3321, Jihar Enugu 2695, Jihar Cross River 2681, Jihar Ekiti 2613, Jihar Plateau 2542, Jihar Kwara 2537, Jihar Niger 2193, Jihar Lagos 2180, Jihar Borno 1822, Jihar Adamawa 1727, Jihar Rivers 1675

Jihar Kano 1545, Jihar Nasarawa 1452, Jihar Katsina 1237, Jihar Gombe State 1218, Jihar Bauchi 1172, Jihar Taraba 1112, Jihar Bayelsa 957, Jihar Kebbi 875, Jihar Ebonyi 865, Jihar Yobe 744, Jihar Sokoto 732, Jihar Jigawa 675, Jihar Zamfara 543, san nan sai wasu mutum 518 da ba a tantance jihoshin da suka fito ba. Jimillar ma'aikatan ya kama 89,511.

Yankin kudu maso gabas na da kaso 18.47% na yawan ma'aikatan, sai yankin kudu maso kudu da kaso 20.15%, san nan kudu maso yamma na da kaso 21. 69%, a yayin da arewa ta tsakiya ta samu kaso 19.95%, arewa maso gabas tana da kaso 10.44%, sai arewa maso yamma da kaso 9.83%.

Source: Naij.com Hausa

Saturday, 2 September 2017

Farare Da Ƙyawawan Mata Yanzu Ake Sawa A Film - Maryam Sangandale

Farare Da Ƙyawawan Mata Yanzu Ake Sawa A Film - Maryam Santander.

Daga : Sharifuddeen Baba, Kano.

Maryam A Baba wacce akafi sani da Maryam Sangandali na ɗaya daga cikin mawaƙan Hausa na zamani da tauraruwarsu ke haskawa a wannan ƙarnin, itama ta halarci taron marubuta na duniya da aka gudanar cikin makon da ya gabata, Kannywoodtoday ta samu zarafin tattaunawa da ita inda ta warware zare da abawar salon waƙoƙiinta.

Sangandale tace ta zaɓi salon waƙa cikin ruwan sanyi ne wanda tace hakan ya fi gamsar da masu sauraro tare da nishaɗantar da masu sauraro. 

Da aka tambayeta ko me ne dalilin da ako da yaushe akafi ganinta da Aminu Alan waqa, sai ta amsa da cewar "ko shakka babu fahimta ce tazo ɗaya dashi, musamman idan aka dubi shima irin salon rera waƙarsa kenan, kuma yana taimakamin wajen gyaramin waƙoƙina tare da yimin gyara, wani lokaci ma ya rubuta min yace ga yadda waƙar zata kasance. Wannan tasa ake ganin muna Kamanceceniya cikin waƙoƙinmu".



Sannan Maryam A Baba ( Mayam Sangandale) ta bayyawa Kannywood today cewar tun ina firamare nake sha’awar waƙoƙi, saboda haka na ƙudurce a zuciyata cewar idan na gama makaranta nima zan bayar da tawa gudunmawar.

Haka kuma an tamabayi Maryam Sangandali shin me yasa bata fita a fina-finan Hausa? 

Sai ta ce "gaskiya iyaka cina waƙa kawai, kasan su fim ana ɗaukar kyawawan mata kuma farare ne, to mu da muke haka sai mu tsaya iya waƙar kawai. Aƙarshe Maryam Sangandali ta bayyana gamsuwarta da wannan taro.

Source : Kannywoodtoday

Ko kunsan Me yasa Hauwa warka ke yawwan fitowa a karuwa a film???

Jarumar fina-finan Hausa, Hauwa Abubakar wacce aka fi sani da Hauwa Waraka, ta ce tana yawan fitowa a mutuniyar banza ne saboda ta nunawa al'umma illar rashin kirki.

"Ina fitowa a matsayin karuwa ko 'yar kwaya ko ballagaza ne saboda na ilimantar da mutane domin su guji zama irin wadannan mutane", in ji Hauwa Waraka, a hira ta musamman da BBC.

Majiyar arewaclass ta samu ce hauwa warkaTa kara da cewa,

"Ban taba karuwanci ba kuma ban taba yin hulda da karuwai ba, amma idan ina taka rawa a matsayin karuwa kai ka ce ni tsohuwar magajiya ce."

A cewar jarumar bai kamata mace da za ta fito a matsayin karuwa "a gan ta sanye da hijabi ba.

Ko kuma macen da ta fito a matsayin 'yar shaye-shaye a gan ta ras kamar mutuniyar kirki ba.

"Shi ya sa za ka gan ni ina keta rashin mutunci a fim kamar da gaske.

Kuma abin da ya kamata kenan."

Hauwa Waraka ta ce sau da dama tana zuwa unguwa mutane suna "cewa wacce irin kwaya ko wiwi ko taba za su kawo min na sha.

Ba su san cewa ban taba shan kayan maye ba; wallahi ko taba ban taba sha ba.

Duk abin da ka ga ni a fim ne".

Da aka tambaye ta kan zargin da ake yi wa 'yan fim na luwadi da madigo, jarumar ta ce akwai bara-gurbi sosai a cikinsu "kamar yadda akwai su a cikin ko da Malaman addini amma bai kamata a yi mana kudin-goro ba.

"Ta bukaci mutane su rika yi musu uzuri musamman ganin cewa su ma mutane ne kamar kowa.

Hauwa Waraka, wacce ta ce tana son yin aure, ta kara da cewa "kai ma wakilin BBC idan kana sona ka fito.

Wallahi aurena ba zai yi tsada ba.

Kai, ni zan hada maka lefe ma
akwati shida idan kana so.

"Ko da yake na san tsoron matarka kake yi kada ka je gida ta ki bude maka kofa"...(dariya).

Source: bbchausa

Monday, 28 August 2017

SHIN DABBA DAYA TA ISARWA MUTUM DA IYALANSA?

SHIN DABBA DAYA TA ISARWA MUTUM DA IYALANSA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Dabba guda daya ta isarwa mutum da iyalansa da wanda yaso  ya sanyashi daka cikin musulmi.

Saboda hadisin Aisha Allah yaqara mata yarda tace :an kawowa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam rago mai qaho, sai yace da ita, bani wuqa, saita kawo masa wuqa, saiya karbi wuqar ya kwantar da ragon sai ya yankashi, sai yace: Da sunan Allah, ya Allah ka karbawa muhammad, da iyalan gidan muhammad, da Al'ummar muhammad, Sannan yai layya dashi.

*Muslim*.

Daka Abu Ayyubal Ansary Allah yaqara masa yarda yace: Mutum azamanin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yana yin layya da Akuya ga kansa da iyalansa, suci naman su ciyar.

*Ibnu Majah da Turmuzi, Albani ya Ingantashi acikin Sahihu turmuzi (1216).*

Idan mutum yayi layya da tunkiya ko akuya ga kansa da iyalan gidansa, ta isarwa duk wanda ya sanya acikin niyyar yankan layyar cikin iyalansa wanda yake raye da Wanda ya Mutu,

Idan bai niyyaci komai ba, ya gamesu koya kebance, duk wanda yake ahlinsane ya shiga, a al'ada ko a luggah.

A al'ada ahlin gida sune matayen mutum da 'ya'yansa da 'yan'uwansa.

A lugga kuma dukkan wani makusancinsa cikin zurriyarsa da zurriyar babansa da zurriyar kakansa, da zurriyar kakan babansa.

Akuya ko tunkiya bata isarwa mutum biyu su hadu su saya suyi layya, saboda rashin ruwaito hakan daka Alqur'ani da Sunnah.

Kamar yanda bai halatta mutum takwas su hadu akan raqumi ko saniya ba,

Amma ya halatta mutum bakwai su hadu akan raqumi ko Saniya.

Amma Tarayya wajan lada wannan ba'a iya kanceba.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.

CREDIT duniyarfatawa

Saturday, 26 August 2017

VIDEO Abin mamaki baya karewa kowa da baiwar da Allah ya masa


       

abin mamaki baya karewa

ku Kalli Abin mamaki baya karewa, kowa da baiwar da
Allah ya masa. DOWNLOAD


Thursday, 24 August 2017

Ban isa aure ba, duka-duka shekaru na 23 - Rahma Sadau

Shahararriyar jarumar nan ta wasannin fina finan Hausa wadda kuma yanzu haka ke a matsayin korarriya a masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau ta bayyana cewa ita yanzu bata da saurayi don kuwa duka-duka shekarar ta 23 a duniya.


          


Jarumar ta yi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da tayi da manema labarai a game da rayuwar ta a dandamalin Kannywood.



Arewarmu.com ta samu a firar ta ta ta jarumar ta kuma bayyana cewar ba za ta taba fidda tsiraicin ta ba duk kuwa da cewar yanzu ta rungumi sana'ar yin fina-finan kudancin kasar nan gadan-gadan.



Haka ma dai jarumar yan asalin garin Kaduna ta kuma dauki dogon lokaci tana sharhi da kuma nuna rashin jin dadin ta game da yadda tace al'ummar hausawa nayi wa harkar tasu mummunar fassara inda ta kara jaddada cewa shifa fim, fim ne ba wai da gaske bane.

Tun farko dai, jarumar ta godewa dukkan masoyan
da suka fito kwarsu da kwarkwata domin taimaka mata.

Credit.  Arewarmu


Thursday, 10 August 2017

Adam A Zango Ya Koma Gona, Noman Tushen Arziki

Shidai wannan hoto da kuke gani na jarumi Adam A Zango ya dora shi a shafinsa na Facebook inda ya rubuta cewa ya koma gona, kasantuwar noma shine tushen arziki.


Adam A Zango ya koma gona

Jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan post na Facebook da shi jarumin yayi inda wasu ke ganin bai kamata a ce jarumin na zuwa gona ba, a yayin da wasu kuma suke ganin hakan yayi daidai.

Da alamu dai jarumin ya dora wannan hoto ne kawai don jin ta bakin jama’a wanda kuma ya samu hakan.

Jaruman fina-finai sukan dora hotuna makamantan wannan don jin ta bakin masoyansu,


Ba Aure Bane a Gabana Kuma Ba Film Bane a Gabana Inji Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya

Aisha Aliyu Tsamiya Ta Fito Fili Ta Bayyanawa Duniya Chewa It a Burin Dake Chikin Ranta, Wanda Yayi Daidai Da Ra'ayinta. jaruma Aisha Aliyu Tsamiya Ta Bayyanawa Shafin BBC Hausa Hakane Bayan Wani Hira Datayi Dasu Cewa, It a Ba Film Bane a Gabanta Kuma Ba Aure Bane a Gabanta.

Tabbas Banida Niyar Yin Aure Yanzu, Duk Da Nasan Hakane Yafi Dacewa Dani a Yanzu.
Kuma Bawai Ina Nufin Na Tsani Aure Bane Ko Kuma Bazanyi Aure Bane A'a, Ina Nufin a Yanzu Karatune a Gabana Ba Aure Ba Kuma Ba Yin Film Ba, Wannan Shine Yadda Na Tsara Yadda Nake So Rayuwata Ta Kasan Che.
Amma Kuma Bance Dole Sai Hakan Ta Faru Ba, Allah Yanayin Duk Yadda Yaso.

Idan Baiso Ba Ko Karatun Ma Bazanyi Ba, In Dai Kwai Na Fadi Ra'ayi Name Sannan Kuma Kowa Yana Da Yadda Ya Tsara Yadda Take So Rayuwarsa Ta Kasanche Cewar Jarumar.

Aisha Aliyu Tsamiya Zata Ci Gaba Da Karatunta a Jami'ar A.B.U Zaria, Domin Yin Degree Political Science.

Read more: http://www.arewarmu.com/2017/08/ba-aure-bane-gabana-kuma-ba-film-bane.html#ixzz4pL4xzxAW